Shugaban Djibouti ya lashe zabe

Hakkin mallakar hoto AFP

Gwamnatin Djibouti ta bayyana shugaba Ismail Omar Guelleh a matsayin wanda ya lashe zaƙen shugaban kasar.

Wannan zai baiwa shugaban damar yin wa'adin mulki na hudu.

Jam'iyyun adawa uku dai sun ƙauracewa zaben.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun zargi shugaban kasar da tauye 'yan cin jama'a.

Djibouti dai tana da muhimmanci ta fuskar tsaro, kasancewar kasar Afirka inda Amurka take da sansanin sojanta.