Austria za ta karbi gidan da aka haifi Hitler

Gidan da aka haifi Adolf Hitler a Austria
Image caption Gidan da aka haifi Adolf Hitler a Austria

Gwamnatin Austria ta baiyana kudirinta na mallakar gidan da aka haifi Hitler a wani mataki na kau da shi daga zama gidan akida na masu ra'ayin Nazi.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida ta Austria yace an yanke wannan shawarar ce bayan shafe tsawon shekaru ana nazarin yadda za'a hana sha'awa sabuwar akidar Nazi.

An haifi Hitler shugaban gwamnatin Jamus ta Nazi a wancan lokaci, a gidan da ke garin Braunau am Inn a watan Afirilu 1889.