Sojoji sun kashe 'yan kunar bakin wake 4

Sojoji Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Najeriya a Maiduguri

Sojojin Najeriya sun ce sun kashe wasu mata 'yan kunar bakin wake da suka saci hanya daga dajin Sambisa za su shiga birnin Maiduguri da nufin kai hari a ranar Juma'a.

Mukaddashin darekatan yada labarai na rundunar sojin kasa ta kasar Kanar Sani Usman Kukasheka ya ce, sojojin sun yi nasar harbe uku a kauyen Madiyari, ta hudun kuwa a kauyen Jimini-Bolori.

Ya kuma ce sojinsu uku sun sami rauni a lamarin.

Rundunar sojin kasa ta kuma ce dakarun kasar sun kama wasu mutane 3 da ake zargin suna da dangantaka da wasu mutane da aka kama da ke kai wa mayakan kungiyar Boko haram abinci.