Matsalar mai ta kusa karewa a Najeriya

A Najeriya yayin da ake cigaba da fuskantar matsalar karancin mai a kasar, kamfanin mai na kasar wato NNPC yace, ana daukar matakan da zasu kawo karshen matsalar.

Kamfanin na NNPC ya kuma ce, ana daf da tabbatar da dukkan matatun mai Nigeria suna aiki sosai.

Tuni dai hukumomin Najeriyar suka bukaci kamfanoni masu zaman kansu su shiga harkar gudanar matatun man kasar.

Malam Garba Deen Muhammad, shi ne kakakin NNPC, kuma yayi karin bayani akan matakan da ake dauka na shawo kan matsalar karancin man.

Matakan sun hada da shigowa da man mai dama daga waje da gyaran bututan man da na matatun kasar da dai sauren su.

An dai shafe dogon lokaci ana fuskantar matsalar mai a Najeriya duk da kasancewar kasar mai arzikin man fetur a Afrika.