'Yan adawa sun koka kan zaben Chadi

kasar Chadi Hakkin mallakar hoto
Image caption Jami'an tsaro na kasar Chadi da ke tsare da masu adawa da gwamnati

Shugaban 'yan adawa a kasar Chadi Saleh Kebzabo ya ce yana da shaida kan magudin da aka tafka a zaben shugaban kasar Chadi da aka yi a ranar Lahadi.

Ana sa ran shugaba kasa mai ci Idriss Deby, shi ne zai sake yin nasara a karo na biyar.

Ya shafe shekaru 26 ya na rike da shugabancin kasar tun bayan da ya yi juyin mulki.

Masu adawa da Mista Deby sun yi zargin cewa ya yi kokarin ganin cewa ba su yi tasiri ba a lokacin yakin neman zabe.

An haramta yin zanga-zangar neman shugaba Deby ya sauka daga kan mulki, kuma ana tsare da masu fafituka a gidan yari.

Ana zargin Mista Deby da fifita kabilarsa ta Zaghawa a kan sauran kabilun da ke kasar.

Masu aiko da rahotani sun ce kasashen yamma sun dauki sojojin Chadi da muhimanci a fadan da ake yi da mayakan Boko Haram a yankin.

Sai dai duk da cewa Chadi kasa ce mai dimbin arzikin mai, rabin yawan alumarta da ya kai miliyan goma sha uku na fama bakin talauci.