Mutane sama da 100 sun hallaka a India

India kerala
Image caption Daya daga cikin mutane da suka ji rauni a wurin Ibada a jihar ta Kerala

Hukumomi a jihar Kerala da ke kudancin India sun umurci kafa kwamitin bincike kan fashewar da kuma gobarar da suka auku a wurin ibada na mabiya hindu da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 100.

Fashewar ta faru ne a wurin Ibada na Puttingal a garin Paravur kuma ana tsamanin wasan wuta da aka yi shi ne ya janyo gobarar.

Fashewar ta kuma sa wani gini ya rufta.

Dubban mutane suka hallara domin kallon wasan wutar kamar yadda ake yi a lokacin biki a kowace shekara.

Jami'ai sun ce an hana mutane izinin gudanar da wasan wutar saboda fargabar rashin kiyayewa.

Fira ministan India, Narendra Modi, ya isa Kerala domin ya ziyarci wurin da hatsarin ya faru.