Zambia na rigakafin cutar kwalara

Hakkin mallakar hoto WSUP JAMES OATWAY PANOS

Ita dai wanan shau-shawa ta riga-kafi da kamuwa daga cutar Kwalara da aka soma yi a Lusaka babban birnin kasar Zambia ita ce mafi girma a duniya, kamar yadda Kungiyar agaji ta Medecins Sans Frontieres ko kuma Doctors Without Borders ta sanar .

Kungiyar MSF da ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Zambia da hukumar lafiya ta duniya na fatan ganin wanan shau-shawa ta kai ga mutane a kala 600,000 a cikin makonni biyu masu zuwa.

Tun dai cikin watan 2 da ya gabata ne aka samu barkewar cutar kwalara a birnin na Lusaka, inda mutane kimanin dari 7 suka kamu da cutar ,daga cikin su guda 20 sun rasa rayukansu.

A birnin na Lusaka dai, sama da mutane milyan daya na rayuwa a cikin wani yanayi na cinkoso ,abun da ya ke hadasa hadarin kamuwa da cutar kwalara a duk lokacin damana.

Rashin tsabtace muhali na daya daga cikin abunbuwan da ke hadasa cutar da yaduwar ta a cikin gaggawa a cikin al'umma.