Cameron ya fidda matakan hana boye kamfani

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Firayi ministan ya fuskanci tuhume-tuhume kan kamfanin da mahaifin sa ya bude a waje, wanda takardun panama suka fiddo.

Firayi ministan Burtaniya, David Cameron ya bada sanarwar sabbin matakan da za su sa da wuya mutane su boye dukiyar da suka samu ta hanyar cin hanci a kamfanonin kasashen waje.

Mista Cameron ya ce a karon farko 'yan sandan Burtaniya da masu tabbatar da bin doka za su rika duba kowa da ke da kamfani a wadannan wurare.

Yawancin yankunan Burtaniya na waje, wadanda wurare ne da ba'a biyan haraji sosai, yanzu za su rika nuna wa mahukuntan Burtaniya.

Firayi ministan na cikin matsin lamba tun da ta bayyana cewa a da yana da hannayen jari a wani kamfanin kasar waje.

Jagoran jam'iyyar adawa ta Labour, Jeremy Corbyn, ya ce mutane na bakin cikin cewa akwai doka daban ga manyan masu arziki da ta sauran mutane.

An samu sauyi a kwanakin da suka gabata, amma ba lallai hakan ya yi wani tasiri na tsawon lokaci ba.