Za a sawa Civilian JTF albashi a Borno

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan kato da goran sun bayar da gudunmawa matuka ga sojoji a yaki da Boko Haram.

A Najeriya gwamnatin jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, da ke fama da rikicin Boko Haram, ta ce ta samar da wani tsari na baiwa 'yan kato da gora, watau Civilian JTF, dubu 20 a matsayin ladan gudanar da cikakken aiki, bayan yaki da kungiyar Boko Haram.

Kwamishinan shari'a na jihar Alhaji Kaka-Shehu Lawan ne ya bayyana wa 'yan jarida haka a Maiduguri.

A hirarsa da BBC kuma kwamishinan ya ce an fidda tsarin ne domin tabbatara da cewa an tanadan wa 'yan kato da goran da suka sadaukar da rayuwansu wajen yaki da Boko Haram, abun yi.

Ya kara da cewa hakan zai kwantar wa al'umma hankali, ganin cewa sun samu abun yi bayan sun rike makamai, ta yadda baza su zamo matsala ga al'umma ba, inda wasu aka sama masu aikin soja, wasu kuma an watsa wasu ayyuka daban-daban.

Alhaji Kaka- Shehu Lawan ya ce Majalisar dokokin jiha ta tsara dokoki kan ayyukan, domin duk gwamnatin da ta biyo bayan wanda zai shude, zai amfana da tsarin a kuma ci gaba shi.