Kotun ECOWAS za ta saurari ƙarar Dasuki

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tun a watan Disambar 2015 ake tsare da Sambo Dasuki

Tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki , ya yi nasara kan gwamnatin ƙasar, bayan da kotun Ecowas ta amince ta saurari shari'arsa kan ƙarar da ya shigar na cewa ana tsare da shi ba bisa ƙa'ida ba.

Kotun ta yi watsi da buƙatar da gwamnatin ƙasar ta gabatar na son ta yi watsi da ƙarar, a wani zama da ta yi a Abuja.

Alƙalin kotun Friday Chijoke Nwoke, ya ce "A ganinmu maganar da Dasuki ya kawo gabanmu batu ne na tabbatar da 'yancinsa na walwala."

Ana tuhumar Dasuki ne da cin hanci da rashawa na wawure miliyoyin daloli da sunan sayo makamai don yaƙar ƙungiyar Boko Haram tun lokacin mulkin Goodluck Jonathan.

Tun a watan Disamba ake tsare da shi duk kuwa da cewa wata babbar kotun Najeriya a Abuja ta bayar da belinsa.

Sai dai Dasuki ya yi watsi da tuhumar da ake masa.