Sirrin rayuwar Bayahudiya 'yar madigo

Chaya, wanda ba sunanta ba ne na gaskiya, wata Bayahudiya ce mai tsattsaurar a ƙida kuma 'yar madigo.

A nan ta bayyana irin fama da ta sha kafin ta gamsu da halin da ta tsinci kanta da kuma dalilin da ya sa za ta boyewa mutane halin da take ciki.

Zan iya rasa komai idan har na bayyana halin da nake ciki. A al'ummata kowa ya san kowa, kuma mun ware kanmu daga sauran al'ummomi.

Al'ummata ta yi Allah wadai da madigo kuma duk wanda ke irin wannan dabi'ar ana masa kallon ba mutumin kirki ba.

Akasarin wadanda muka taso da su suna tunanin ko me kuma zan iya aikatawa da ya fi wannan?

Mutane kadan ne suka yarda cewa zan iya zama mai karfin addini kuma idan har na bar al'ummar Heradi hakan na nufin zan rasa aikina da iyali da kuma yaran da zan haifa.

Mutane suna nuna kamar basu san halin da nake ciki ba.

Hakkin mallakar hoto bb

Akasarinsu suna yi kamar basu san da cewa ana samun masu luwadi da madigo ba a rayuwa.

A lokacin da nake makaranta na shaidawa wani Malamin addini cewa ni 'yar madigo ce, amma a lokacin sai ya shaida min cewar "Lokaci ne kawai, yara mata da dama suna samun kansu a irin wannan halin."

Ba a hada mata da maza a makarantarmu da zarar mun kai shekara uku da haihuwa. Wasu iyalan ma masu tsattsauran ra'ayi su kan hana wa da kanwa su yi wasa tare.

Na fara madigo a lokacin da nake da shekaru 12 a duniya, amma kuma sai ake ganin abu ne da zan bari a gaba.

Da na kara wayo sai 'yan ajinmu a makaranta suka fara kira na da 'yar madigo duk da cewa a lokacin bana komai.

Abin ya cigaba da damuna, a dalilin haka ne na shaidawa mahaifiyata halin da na ke ciki a lokacin da na yi shekara 16, amma sai ta nuna min cewa yin hakan haramun ne kuma tun daga lokacin bamu kara yin maganar ba.

Ba da dadewa ba sai iyayena su ka fara neman wanda zasu hada ni aure da shi.

A kan samu wanda zai hada aure a irin yara mata da suke irin wannan dabi'ar. Wanda ya hada din ya kan samu har fam dubu 15. Sai dai iyayena sun yanke hukunci za su samo min miji da kansu.

Daga sama min mijin sai aka gayyato shi cin gidanmu. Iyayensa da iyayena sun tattauna sai kuma suka tafi suka barni da wanda zan aura din.

Duk da cewar na samu sa'ida a lokacin da aka sama mijin da zan aura, na yi fatan cewa hakan zai sa na yi watsi da dabi'ar.

Amma wata guda kafin aurena sai na hadu da wata yarinya.

Amma kuma sai muka rabu daf da za a yi bikina. Na zaci zan iya mantawa da abubuwan da na yi a baya.

Ana bamu karfin gwiwar mu haifi yara domin mu inganta iyali kuma bayan an yi auren na samu juna biyu da wuri.

Ana sa mana ran haifar yara takwas zuwa tara kuma sai na yi ta samun ciki akai-akai.

Amma kuma ina yawan tunanin dabi'ar tawa, sai wata rana ina tafiya a kan wani titin da baya bullewa a wani wuri, sai nake ta jin hayaniya da yawa a cikin kaina da har yasa na fara ihu ina cewa "Ni 'yar madigo ce, ni 'yar madigo ce da karfi sosai."

A lokacin sai na ji ya kamata na yi wani abu a kan dabi'ar tawa, daga bisani sai na shaidawa mijina.

Ina ga duk za mu yi asara idan har muka ce za mu rabu a don haka gwara na zauna tare da mijina.

Mata da dama suna koyarwa a makarantu masu zaman kansu ko kuma su yi aiki a matsayin sakatare.

Ana sa ido a kan yadda muke suturce jikinmu, saboda bai kamata mu bayyana al'aurarmu ga wani ba sai dai mazan da muke aure.

Mutane suna cewa ni mai taurin kai ce. Wasu suna dora alhakin rashin kintsina a kan dabi'ar da nake yi. Suna cewa siket dina ya yi gajarta. Gashina ma abu ne da suke tattaunawa a kai.

Yanzu ina ga na fara bin ka'idojin da addininmu ya gindaya wajen suturce gashi amma har yanzu akwai sauran abubuwa da dama da ya kamata na yi wajen bin ka'idojin addinina.

Ita a ganinta mutane da dama suna Allah wadai da dabi'ar, amma a cewarta basu da hurumin yin hakan. Ta ce imani ba daga wurinsu yake ba.

Ta ce zan cigaba da addini a. Zan kasance Bayahudiya, wani bangare ne na rayuwata, kamar sauran abubuwan da suka danganci rayuwata.

Ta ce na sama masa wani sabon suna, suna kiran addinin da cewa "Yahudawa masu akidar zamani da kuma masu tsohuwar akida." Amma ni ina kiransai Yahudanci na gaskiya.

Ta ce ban sani ba wata kila nan da shekaru 40 zai zama wani abu da mutane za su yi fafutuka a kansa.