Gwamnatin jihar Kaduna ta binne mutane 347 a rikicin Zaria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar 'yan uwa musulmi mabiya shi'a sun ce ba su amince da adadin da gwamnati ta bayar ba.

A Najeriya, gwamnatin jahar Kaduna ta ce mutane 347 ne aka halaka a Zaria yayin rikici tsakanin 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi mabiya akidar shi'a da sojoji a watan Disembar shekarar da ta gabata.

Gwamnatin jahar wacce ta bada bahasinta a gaban kwamitin shari'a da ke binciken rikicin, tace an binne gawarwakin mutanen 347 ne gaba daya a wani wuri a Mando da ke wajen garin Kaduna bayan samun izinin babbar kotun jahar.

Sai dai kungiyar 'yan uwa musulmi mabiya shi'a sun ce ba su amince da adadin da gwamnati ta bayar ba.

Kazalika kungiyar ta 'yan shi'a ta ce ba su amince da dalilan gwamnati ba na yiwa mabiyan nata janaizar gaba daya.