Macedonia :An harbi 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto Reuters

A cewar ƙungiyar agaji ta Medecins sans Frontieres , kimanin 'yan gudun hijira 300 ne suka samu rauni.

Wannan lamari ya wakana bayan da 'yan sanda suka harba hayaƙi mai sa ƙwalla a cikin taron jama'ar da ke shiga kasar ta Girka.

Wani jami'i a hukumar ta MSF ya sanar da cewa 'yan gudun hijira ɗari biyu ne aka yi wa magani game da matsalar lumfashi.

Wasu guda 30 kuma sun samu rauni ne sanadiyar harbin da harsashen robba.

Matasa 'yan gudun hijira sun jefi 'yan sandar Macedonia ne a lokacin da 'yan sandar suka hana su ƙetara shingen da aka saka kan iyaka.

Goerge Kyritsis kakakin gwamnatin Girka, wanda ke magana kan 'yan gudun hijira:

''ya ce amfani da karfi da aka yi kan yan gudun hijirar bai dace ba'' .