"Ana damfara da sunan 'yan gudun hijirar Boko Haram"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kiyasta cewa fiye da mutane miliyan biyu ne rikicin Boko Haram ya tilasta musu barin gidajensu a Najeriya.

Wasu kungiyoyin ba da agaji a Najeriya sun yi zargin cewa ana amfani da mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a yankin arewa maso gabashin kasar don damfarar kasashen duniya da ma kungiyoyi masu zaman kansu ta hanyar karkatar da taimakon da suke bayarwa.

Wannan zargin na zuwa ne yayin da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a kasar ke cewa sun dukufa domin tallafa wa 'yan gudun hijirar da kuma sake tsugunar da su.

Dr Fatima Zanna Gana, shugabar kungiyar Purple Heart Foundation, wacce ke tallafa wa 'yan gudun hijirar a jihar Borno ta shaida wa BBC cewa ana ci da gumin 'yan gudun hijirar ta hanyar yin awon gaba da miliyoyin daloli da sunan tallafa musu.

An dai kiyasta cewa fiye da mutane miliyan biyu ne rikicin Boko Haram ya tilasta musu barin gidajensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.