Obama ya yi nadamar rikicin Libya

Image caption Shugaba Barack Obama na Amurka

Shugaban Amurka, Barack Obama ya ce rashin shiryawa abin da ya biyo bayan hambarar da shugaban kasar Libya Mu'ammar Gaddafi, shi ne kuskure mafi muni da fadarsa ta yi.

Gidan talabijin na Fox da ke Amurka ne ya yi wa mista Obaman tambayoyi a kan abubuwan da gwamnatinsa ta yi mafi muni da kuma abu mafi kyau.

Ya ce, duk da haka shiga tsakani a rikicin na Libya da kasarsa ta yi abu ne da ya dace".

Amurka da wasu kasashen sun kai hare-hare ta sama da nufin kare fararen hula a lokacin rikicin nuna adawa da gwamnatin Gaddafi a shekarar 2011.

Sai dai bayan an kashe tsohon shugaban Libyan, sai kasar ta fada cikin tashin hankali da rudani, inda ta kai har masu tayar da kayar baya suka karbe mulki, kuma aka kafa gwamnatoci biyu da majalisunsu da ke hamayya da juna.

Gwamnatin hadin gwiwa wanda Majalisar Dinkin Duniya ke goyon baya ta isa Tripoli, amma tana jira ta karbi mulki.