"An binne 'yan Shi'a 347 a kabari daya a Nigeria"

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya, gwamnatin jihar Kaduna ta ba da ba'asi a gaban kwamitin bincike kan rikicin 'yan shi'a da sojoji a ranar Litinin.

Gwamnati ta ce mutane 347 ne aka binne a kabari É—aya.

Sai dai kuma 'yan Shi'ar sun musanta adadin da cewa ya fi haka.

Sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Balarabe Lawal ne ya bayyana a wajen wani zaman bayar da ba'asi a gaban kwamitin binciken da aka kafa .

A karo na farko da gwamnati ke fayyace lamarin, sanarwar ta ce an binne gawarwakin 'yan shi'an ne a asirce.

A bayanin sakataren, wanda shi ne jagoran Mutane shidda da suka tabbatar da lamarin, ya ce an binne gawarwaki 191 da aka dauko daga sansanin soja da ke Zaria, a unguwar Mando da ke Kaduna.

Ya kara da cewa akwai karin gawarwaki 156 da aka dauko daga asibitin Ahmadu Bello da ke Zaria, wadanda su ma aka kai Mandon.

Jami'in gwamnatin ya ce gawarwakin na matasa ne 'yan kungiyar 'yanuwa Musulmi, watau Islamic Movement(IMN), wadanda ya ce an zarga da neman kai wa tawagar babban hafsan sojojin kasar, Laftanan-Janar Tukur Buratai, hari a ranar 12 ga watan Disambar shekarar 2015.

Malam Lawal Balarabe dai bai bayyana ko iyalan mamatan sun samu damar ganinsu kafin a kai ga binne su ba.