Me zai sa Daily Mail ko wani sayen Yahoo?

Kamfanin Yahoo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kamfanin Yahoo

Masu saka hannayen jari basu gamsu ba, saboda ana kara samun rahotanni kan rufe wasu daga cikin harkokin kasuwancin kamfanin na Yahoo.

Tun bayan da hukumar tara kudaden haraji ta Amurka ta toshe hanyoyin sayar da hanayen jarin kamfanin na Yahoo a harkokin kasuwancin kasar China, jagorar kamfanin Marissa Mayer ta koma ga zabar bin hanyar sayar da wasu bangaroriin kasuwancin kamfanin.

Tun a cikin watan Fabrairu ne ake danganta gwamman kamfanonin Amurka da kasancewa masu shiga cinikin na Yahoo.

Amma kuma jagoran kamfanin jaridar Daily Mail da ke Birtaniya ya tabbatar da cewa kamfanin na tattaunawa da wasu mutane da ba a bayyana sunayensu ba kan su shiga cikin harkar- lamarin da ta zo wa da mutane da dama mamaki.