"Dole sojoji su fadi gaskiyar lamarin Shi'a"

Hakkin mallakar hoto AP

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta ce dole a yi binciken gaggawa kan lamarin da ya bayyana, game da rahoton da gwamnatin jihar Kaduna ta bayar na jana'izar bai-daya da aka yi wa 'yan Shi'a.

Jami'an gwamnatin Kaduna sun bayar da tabbacin ne a wani ba'asi kan rikicin da ya faru daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Disambar shekarar 2015 a Zaria, wanda ya tabbatar da binciken da kungiyar ta Amnesty International take gudanarwa.

Daraktan kungiyar a Najeriya M.K Ibrahim, ya ce, "Wannan bayani maras dadin ji da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar na cewa an harbe daruruwan 'yan Shi'a, aka kuma binne su a kabari daya, zai taimaka wajen gano wadanda suka aikata wannan ta'asa lokacin shari'a."

Ya kara da cewa, dole a kafa tsaro a wuraren kabarin, domin gudanar da sahihin bincike kan lamarin.

"Dole a tono kabarin, kuma rundunar sojin Najeriya ta bayyana wadanda ke da alhaki domin a hukunta su, ko a sallame su." In ji M.K Ibrahim.

Amnesty International ta soma gudanar da bincike game da rikicin Zariyar tun watan a Janairun shekarar 2016, inda suke tattara rahoton da zasu wallafa nan ba da dadewa ba.