'Yan Boko Haram sun shiga cikin al'umma

Hakkin mallakar hoto Getty

Rundunar sojin Nigeria ta ce mayakan Boko Haram suna ta bazama cikin ɓangarorin ƙasar sakamakon hare-haren sama da na kasa da sojoji ke kai musu da kuma rusa sansanoninsu da rundunar ke yi dajin Sambisa.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, kakakinta Kanal Sani Usman Kuka-Sheka ya ce, a domin haka ne ake jan hankalin al'umma da su zama masu sanya ido da yin taka tsan-tsan a duk inda suke.

Sanarwar ta kuma ce ana buƙatar 'yan Najeriya da su sanar da hukumomin tsaro duk wani mutum da basu yarda da shi ba ko suke zarginsa, domin ɗaukar mataki nan da nan.

Ta kara da cewa sojojin ƙasar za su cigaba da wannan yaki da mayaƙan Boko Haram ba gudu ba ja da baya har sai sun tabbatar da cewa babu ɓurɓushin mayakan.