Dilma ta zargi mataimakin ta

Image caption Dilma Rousseff shugabar kasar Brazil na fuskanta tsigewa daga majalisar dokokin kasar.

Shugabar kasar Brazil, Dilma Rousseff, wacce ke fuskantar tsigewa a majalisar dokokin kasar, ta zargi mataimakinta da hannu a shirin kifar da ita.

Da take magana cikin fushi a Braslia, babban birnin kasar, Mrs Rousseff ta ce yanzu makiyanta sun fito fili suna kokarin kifar da zababbiyar shugabar kasa.

Shugabar ta yi magana ne kan wani sako na murya da mataimakin shugaban kasar, Michel Temer, ya fitar ranar litinin, inda ya yi magana kamar ma an riga an tsige tan.

Bayanin nasa ya fito ne sa'o'i gabanin wani kwamitin majalisar dokokin ya kada kuri'a ta neman majalisar wakilai ta tsige shugaba Rousseff.