Brazil: Ana shirin tsige shugaba Rouseff

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Dilma Rouseff ta Brazil

Kwamitin Musammman na majalisar dokokin Brazil ya kaɗa ƙuri'ar amincewa da tsige shugaba Dilma Rouseff, bayan wata zazzafar muhawara.

Yanzu haka za a kuma sake gabatar da batun don kaɗa cikakkiyar ƙuri'a a zauren majalisar dokokin inda ake buƙatar kashi biyu bisa uku mafi rinjaye kafin a cigaba da batun tsigewar.

Kwamitin musamman kan batun tsige shugabar ya kaɗa ƙuri'u 38 kan 27 don amincewa da tsige shugaba Rouseff din.

Ana dai zargin shugaba Rouseff da yi wa tattalin arzikin ƙasar karan tsaye, da kuma badaƙalar cin hanci da rashawa a kamfanin mai na Petrobras na gwamnatin ƙasar.

Shugaba Rousseff ta musanta zarge-zargen tana mai cewa zargin da ake yi mata ba su kai na laifin da za a tsige ta ba.

Nan gaba a cikin makon gobe ne ake sa ran za a kaɗa cikakkiyar ƙuri'a tsakanin mambobin majalisar mai yawan mutane 513, inda ake bukatar biyu bisa ukun 'yan majalisar kafin a je ga batun tsige shugabar a majalisar dattawa.

Hakan kuma na nufin akwai yiwuwar dakatar da shugaba Rousseff na tsawon kwanaki 180, yayinda majlaisar dattawan ke cigaba da zaman shirin tsigewar.