China za ta ba wa Nigeria bashin dala biliyan 6

Kasar China ta bai wa Najeriya bashin kimanin biliyan 6, domin inganta tsarin gine-gine da abubuwan more rayuwa a kasar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Dr Jibrin Ibrahim, mai sharhi ne kan harkokin yau da kullum a Najeriya, Aminu Abdulkadir, ya tuntube shi domin jin ko ya yake kallon bashin da Najeriyar ta samu daga Chinar?

A ranar Lahadi ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki a kasar, inda ya gana da takwaransa na China Xi Jinping.

Hukumomin Najeriya dai sun ce manufar ziyarar ita ce karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu a yunkurin gwamnatin ƙasar na fadada hanyoyin samun kuɗin shiga, da bunƙasa harkar noma, da hakar ma'adinai.

Sun kuma ƙara da cewa shugabannin ƙasashen biyu za su kammala cimma wasu yarjejeniyoyi da dama da suka danganci habaka cinikayya, da karfafa dankon zumunci ta fuskar tattalin arziki.

Da ma dai wasu 'yan Najeriya sun ja hankali game da cewa dalilin ziyarar shi ne batun karbo bashi don cike giɓin kasafin kuɗin kasar na bana.

Mista Femi Falana wani lauya ne mai zaman kansa, kuma mai fafutuka a Najeriyar, ya rubuta wa ministar kuɗi ta ƙasar wasiƙa yana jan kunnen gwamnatin kada ta kuskura ta karɓo bashi.