Abubuwa 5 da ya kamata ka sani kan shugaba Dilma Rousseff ta Brazil

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff, ta gaza shawo kan yunkurin da ake yi na tsigeta daga kan mulki, bayan wani kwamitin 'yan majaliasar dokokin kasar ya amince a cigaba da yunkurin tsigetan.

Kwamitin 'yan majalisar dokoki mai yawan mutane 65 sun kaɗa ƙuria a wannan mako, wadda mutane 38 zuwa 27 suka bayar da shawarar a tsigeta a kan zargin ta yi rufa-rufa a kan alkaluman asusun gwamnatin domin boye gibin da ke cikin asusun.

Za a sakawa 'yan majalisar wakilai ido a kan zaben, wanda za a yi ranar 17 ko 18 ga watan Afrilu.

Lamarin ya jawo rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan kasar Brazil din inda 'yan sanda a kasar suke shiri a kan wata zanga-zanga da za a yi Brasillia, babban birnin kasar.

'Yan majalisa masu adawa suna so su tsige shugaba Dilma Rousseff a kan zargin yin rufa- rufa a alkaluman kudade da ke asusun gwamnatin domin boye gibin da ke cikinsa.

Miss Rousseff, wace ta musanta zargin, ta ce lamarin na iya jawo juyin mulki.

Amma ya aka yi 'yar fursunar siyasa ta zama shugabar daya daga cikin kasashe masu fada aji na Kudancin Amurka?

Hakkin mallakar hoto AFP
Ita ce shugabar kasa mace ta farko a Brazil

Dilma Roussef ce mace ta farko da aka zaba a matsayin shugaba a Brazil.

An san ta ne sosai a matsayin mai 'yar gani kashenin Luiz Inacio Lula da Silva, tsohon shugaban Brazil din wanda aka fi saninsa da Lula.

A shekarar 2014 ne ta sha da kyar a zaben shugabar kasa a karo na biyu a kan abokin hamayarta Aecio Neves.

Gwamnatinta ta fuskanci zanga-zanga

Magoya bayan Miss Rousseff suna yabonta a kan tafiya da kowa da kowa da kuma tsarinta na tallafawa mutane wanda mutanen Brazil miliyan 36 suka amfana da shi.

Sai dai 'yan Brazil din da dama sun yi adawa da goyon bayan da gwamnatin ta bayar na kashe kudade da yawa da aka yi a kan al'amuran wassani kamar na wasan cin kofin duniya na shekarar 2014, a lokacin da ake cigaba da fuskantar rashin dai-daito da kuma talauci.

A watan Yunin shekarar 2013 ne aka yi kiyasin cewa masu zanga-zanga kusan miliyan sun hau kan tituna domin nuna adawa ga karin kudin motar haya.

Zanga-zangar ta bazu a kasar baki daya inda mutane suka nuna fushinsu a kan cin hanci da rashin ingantance tsaro da sufuri da kuma tsarin kiwon lafiya.

Miss Rousseff ta ce za ta duba wadannan batutuwa amma kuma ta dage a kan cewa ba da kudaden jama'a aka yi amfani ba wajen wasan cin kofin duniya .

Hakkin mallakar hoto AFP
Ana ganinta mace mai kamar maza a Brazil

An yi mata lakabi da "Mace mai kamar maza," Miss Rousseff tana komai ke-ke da ke-ke kuma tana da saurin fushi - kuma tozarta ministocinta a bainar jama'a da ta ke yi yasa ana shakkarta.

An fara zabarta ne a shekarar 2010 kuma an saka sunanta a matsayin ta bakwai a jerin matan da suka fi yin fice a jerin sunayen matan da suka yi fice a duniya a mujallar Forbes na shekarar 2015.

Da mamba ce a kungiyoyin masu tada kayar baya na karkashin kasa

An haifeta a shekarar 1947 kuma ta girma a gidan iyalai masu rufin asiri a Belo Horizonte.

Mahaifinta, Pedro Rousseff, a da dan kwaminisanci ne kuma dan ci-ranin Bulgaria ne.

Duk da cewar ta so ta zama mai yin rawar Ballerina, ta yi watsi da hakan bayan ta shiga kungiyar masu sassaucin ra'ayi a kan mulkin kama karyar sojojin Brazil wadanda suka kwace mulki a shekarar 1964.

A shekarun 1970 aka kamata aka tsare a gidan yari na tsawon shekara uku. An yi mata azaba da ta hada da sa mata wutar lantarki sakamon rawar da ta taka a kungiyoyin masu tayar da kayar baya na karkashin kasa.

A lokacin da ake shari'arta, an kirata da "Malamar sama da fadi."

Hakkin mallakar hoto EPA
Ta yi nasarar lashe zaben shugaban kasa guda biyu.

A shekarar 2010 ne aka yi mata tiyata domin sauya wasu bangarorin jikinta da kuma karawa hakoranta haske domin ta samu goyon bayan mutane.

Ba ta sanu kuri'u isassu ba a zagaye na farko da za su taimaka mata wajen lashe zaben shugabar kasa, amma kuma ta yi nasara a kan Jose Serra ta jam'iyyar Social Democracy Party, a zagaye na biyu da kuri'u sama da kashi 56 cikin dari.

A baya-bayan nan an yi zanga-zanga da dama a kan cin hanci, inda masu zanga-zangar suke zargin jam'yyar ma'aikata mai mulki da hannu a karbar hanci a kamfanin mai na kasa na Petrobras.

Miss Rousseff ta musanta zargin hannunta a ciki kuma an cireta daga binciken da Antony janar ke yi.