'Yan kasuwar Najeriya ne ke sa tsadar shinkafa - Kwastam

Hakkin mallakar hoto Nigeria Customs
Image caption 'Yan kasuwar Najeriya na dora alhakin tashin farashin shinkafa da hana shigar da shinkafar ta kan iyakokin kasa.

Hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya wato kwastam ta zargi 'yan kasuwar ƙasar da cewa su ne ke haddasa tsadar shinkafar da ake fama da ita a yanzu haka a ƙasar.

Hukumar ta kwastam ta ce 'yan kasuwar sun yi amfani da haramta shigar da shinkafar da aka yi ta iyakokin tsandauri, inda suke cewa an haramta shigo da shinkafar ne baki daya.

Su dai 'yan kasuwar ƙasar na ɗora alhakin tashin farashin da shinkafa ta yi kan matakin da hukumar ta hana fasa ƙwauri ta ɗauka na hana shigar da shinkafar ta kan iyakokin ƙasa.

A farkon wannan shekarar ne hamshakin mai kudin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya ƙaddamar da shirinsa na bunƙasa harkar noma a jihar Jigawa da ke Najeriya.

Shirin dai wani bangare ne na yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin gwamnatin jihar Jigawa da kuma kamfanin na Dangote.

An ware kadada 20,000 a jihar Jigawa, da za a yi amfani da su wajen gagarumin aikin noman shinkafar zamani, inda za a samar da shinkafa mai yawa don bunkasa samar da abinci a kasar.