Tattalin arzikin yankin Sahara zai ragu — IMF

Image caption Faduwar farashin man fetur na jawo raguwar tattalin arzikin wasu kasashen

Ana hasashen tattalin arzikin yankin kudu da hamadar saharar Afrika zai ragu da kashi uku cikin 100 daga kashi 3.4 a shekarar 2015, sakamakon faduwar da farashin man fetur ke cigaba da yi.

Wannan hasashe ya fito ne a wani rahoto da asusun bayar da lamuni na duniya IMF ya fitar, inda ya ce faduwar farashin man fetur din na shafar manyan kasashe masu samar da man kamar Najeriya da Angola, duk da cewa tasirin ya ragu zuwa yanzu.

Hasashen habakar tattalin arzikin Najeriya ya yi kasa da kashi 2.2 cikin 100 a shekarar 2015, yayin da na Angola ma zai iya raguwa da kashi 2.5 daga kashi uku cikin 100.

Sai dai tasirin faduwar farashin man a kan kasashen yankin da suka fi samar da shi bai yi yawa ba sosai kamar yadda aka yi tsammanin, domin yawancin wadannan kasashe suna fitar da wasu sauran kayayyakin kasashen waje.

R<span >ahoton ya ce an kiyasta tattalin arzikin kasashen Afirka kudu da Sahara zai bunkasa da kashi hudu cikin dari sakamakon 'yar habakar da aka samu a farashin kayayyaki da kuma aiwatar da wasu manufofi a lokacin da ya dace.