Sudan ta Kudu: Reik Machar ya dawo gida

Yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu da jagoran 'yan tawaye Reik Machar

Jagoran 'yan adawa na Sudan ta Kudu Riek Machar ya dawo kasar, a wani matakin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnati da 'yan tawaye.

Mr Machar din zai karbi sabon mukaminsa ne na mataimakin shugaban kasa kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

Mai magana da yawun Mr Machar ya tabbatarwa da BBC cewa, yanzu haka yana na nan a helkwatar 'yan tawaye dake gabashin kasar kusa da kan iyakar ta da kasar Ethiopia ko kuma Habasha.

Ana kuma sa ran zai wuce zuwa Juba babban birnin kasar a ranar Litinin a karon farko cikin fiye da shekaru biyu.

Takaddama tsakanin Mr Machar da shugaba Salva Kiir ta haddasa mummunan yakin basasa a kasar cikin watan Disambar shekara ta 2013.

Dubannin daruruwan mutane ne aka hallaka yayin tashin hankalin, kana fiye da miliyan biyu suka rasa matsugunansu.

Ana sa ran sojoji da yansanda za su samarwa da Mr Machar kariya, wanda ya ce ba zai zo ya karbi mukamin nasa ba har sai an daukar masa matakan tsaro.

Duka bangarorin biyu sun sha karya yarjejeniyar zaman lafiyar a cikin shekaru, don haka har yanzu akwai alamun rashin yarda a cikin sabuwar gwamnatin.