Abubuwa biyar kan dangantakar Nigeria da China

Hakkin mallakar hoto Garba Shehu
Image caption Shugaban Najeriya Buhari na ziyara a China don kulla alakar cinikayya
Alakar da ke tsakanin Nigeria da China ta girmama ta hanyar fadada harkokin kasuwanci da dabarun hadin kai tsakaninsu.

China ta dauki Najeriya a matsayin daya daga cikin kawanyenta na kut, kuma abokiyar harka.

Haka kuma China na daga cikin abokan huldar Najeriya a kan kasuwanci da fitar da kayayyaki.

Sakamakon wata kuri'ar jin ra'ayi da BBC ta gudanar a shekarar 2014, ya nuna cewa kashi 85 cikin 100 na 'yan Najeiya na kallon alakar kasarsu da China a matsayin wani abu mai fa'ida, inda kashi 10 ne kacal suke kallon rashin amfanin dangantakar, al'amarin da ya sa Nigeria ta zamo wata 'yar gani kashenin China.

Ga dai wasu abubuwa biyar da za su kara nuna maka karfin alakar da ke tsakanin kasashen biyu:

1. Dangantakar shekaru arba'inA watan Fabrairun shekarar 1971 ne Najeriya da China suka kulla dangantakar diflomasiyya. A wannan shekara ne dai Najeriya da sauran kasashe masu tasowa a nahiyar Asiya da Afrika da Latin Amurka suka taimakawa China wajen samun tagomashin da take nema a duniya, duk kuwa da irin adawar da Amurka ke nunawa kan hakan.

A cikin shekaru 30 da suka biyo baya, alakar kasashen biyu ba ta haifar da wata gagarumar nasara ba ta fannin tattalin arziki, saboda a yayin da China ke samun ci gaba wajen zamowa kasa mai karfin tattalin arziki, ita kuwa Najeirya sai shekarun 1980 da na 1990 suka zame mata na juyin mulkin soji daban-daban.

Sai dai a lokacin mulkin Janar Sani Abacha ya kara karfafa dangantakar kasashen, inda har aka samar da cibiyar kasuwanci ta Najeriya da China a shekarar 1994. Dangantakar tasu bata kara kankama sosai ba sai bayan dawowar dimokradiyya a Najeriya.

Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ma ya sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama tsakanin kasarsa da China a lokacin mulkinsa. A shekarar 2006 kasashen biyu suka sanya hannu kan saka jari da China zata yi a bangarorin man fetur da wutar lantarki da harkokin sadarwa da kuma masana'antu.

Kazalika, wannan dangantaka ta cigaba da habaka ta fuskoki da dama a lokutan mulkin shugaba 'Yar adua da Goodluck Jonathan.

2. Rashin daidaton cinikayya tsakanin kasashen biyu

Mu'amalar cinikayya ta kara girma ta hanyoyi daban-daban tun bayan da Najeriya da China suka sanya hannu kan wata yarjejeniya a shekarar 2001.

Yawan adadin kudin kasuwancin ya kai dala biliyan 17.7 a shekarar 2010. Duk da cewa fitar da kayayyaki da Najeriya ke yi zuwa China ya rubanya, amma bai ko kama kafar wanda China ke shigarwa Najeriya ba. Wannan al'amari ya kawo rashin daidaito kan harkar cinikayya tsakaninsu.

A shekara ta 2000 China ce ke da kashi 66.7 cikin 100 na shigo da kayayyaki Nigeria, yayin da a shekara ta 2010 yawan ya kara ninkawa zuwa kashi 87.3 cikin 100.

A shekarar 2010 ne Najeriya ta zama kasa ta hudu daga cikin manyan kasashen da China ta fi mu'amala da su a Afrika.

Kashi daya bisa uku na kasuwancin da China ke yi a Afrika ya ta'allaka ne ga Najeriya.

3. Bunkasar tattalin arzikin Najeriya da zuba jarin China
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption China ta yi nisa wajen harkar tama da karafa da sarrafa ma'adinai

Matakan da Najeriya ke dauka domin bunkasa tattalin arzikinta da kuma dumbin arzikin da take da shi na man fetur da iskar gasa, na daga cikin abubuwan da suka jawo hankalin masu saka jari daga China.

A cewar China, Najeriya ce kasa ta biyu da ta fi saka jarinta a can baya ga kasar Afrika Ta Kudu tsakanin shekara ta 2003 da ta 2009. Adadin kudin da China ta saka jari a Najeriya ya kai dala biliyan 1.03, yayin da ta saka jumlar dala biliyan 9.3 a nahiyar.

An yi hasashen cewa saka jarin China a Afrika zai kai dala biliyan 50 a shekarar 2015.

4. Sayen mai daga Nigeria
Hakkin mallakar hoto Garba Shehu

A shekaru goman da suka gabata, China na sayen kashi daya bisa uku na man fetur dinta ne daga kasashen Afrika.

Najeriya ce kasa ta shida da china tafi sayen danyen man fetur daga wajenta a nahiyar Afrika, China na sayen kashi biyu cikin 100 ne kawai na man da take saya daga Afrika a wajenta.

Haka kuma China na sayen kashi 1.6 cikin 100 ne na adadin man da Najeriyar ta sayar a shekarar 2010, inda bai ko kama kafar yawan da Amurka ta saya ba.

5. Alakar zamantakewa da al'adu
Hakkin mallakar hoto Tim Maughan
Image caption Kayayyakin China na kasuwa a Nigeria

Alakar tattalin arziki tsakanin China Da Najeriya ya kawo karfafa alaka ta zamantakewa da ala'adu tsakaninsu.

Duk da cewa ba a samu wani tabbatacciyar kididdiga ba amma an yi kiyasin cewa 'yan kasar China 50,000 ne suke zaune a Najeriya. Yawan 'yan Chinan na karuwa ne sakamakon alakar tattalin arziki da take habaka. A shekarun 1960 da na 1970 ne 'yan kasar Hong Kong da Taiwan da kuma China suka zo Najeriya inda suka kafa ayyukan masana'antu musamman ma na tufafi a Kaduna.

Da yawansu sun fara barin ayyukan suna barin kasar saboda gasar da aka fara samu ta shigo da kaya masu sauki daga wajen.

Kusan ana samun 'yan kasar China a kowacce babbar kasuwa da ke manyan biranen Najeriya, inda ta kai a yanzu har sun fara mamaye kananan garuruwa ma.

Daya daga cikin manyan wuraren kasuwanci n China a Najeriya shi ne Chinatown da ke birnin Lagos wanda aka gina a shhekarar 2004, wanda yake da kusan shaguna 120 inda ake sayar da kayayyakin amfani da ake shigo da su daga China.

Amma mafi yawan 'yan Najeriya da ke China kuwa, 'yan kasuwa ne da ke zuwa su zauna na dan lokaci kuma sun fi mayar da hankali ne kan manyan masana'antu.

Wani jami'in ofishin jakadancin Najeriya ya kiyasta cewa akwai 'yan Najeriya kusan 3,000 a yankin Guangdong kawai.

Kazalika, 'yan Najeriya na kuma zuwa China don yin karatu da kuma koyar da turanci.

An kuma kiyasta cewa akwai 'yan Najeriya 700 a gidajen yarin China wadanda yawanci ake tuhumarsu da laifukan keta dokar shige da fice da zamba da safarar miyagun kwayoyi, al'amarin da ya jawo rashin yarda tsakanin 'yan kasashen.