Taiwan za ta yi karar 'yan sandan Kenya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mahukuntan Taiwan din sun ce za su yi karar Kenya
Mahukunta a Taiwan sun zargi 'yan sandan Kenya da amfani da hayaki mai sa kwalla da bindigogi domin tilasta wa 'yan Taiwan su 37 hawa jirgi zuwa China.

Jami'an Taiwan sun ce wasu daga cikin mutanen sun killace kansu a cikin wani kurkukun 'yan sanda, amma aka fasa wata katanga suka kamo su.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajan Taiwan Antonio Chen, ya ce za su yi hayar lauyoyi su shigar da kara a kan ma'aikatar 'yan sandan Kenya.

Wannan shi ne rukuni na biyu na mutanen da ke dauke da fasfon Taiwan da ake mayar wa China cikin kwanaki biyar.

An wanke wasu daga cikinsu daga aikata laifukan da suka shafi zamba.

Taiwan ta zargi China da sa matsin lamba kan Kenya, tana mai cewa Beijing tana sace mata 'yan kasa.