Nigeria: 'Yan bindiga sun kai hari Taraba

Rahotanni daga jihar Taraba a arewa maso gabashin Nijeriya na cewa mutane arba'in da hudu sun rasa rayukansu wasu da dama kuma suka jikkata a wani jerin hare-haren 'yan bindiga.

Lamarin ya faru ne a wasu kauyuka dake cikin karamar hukumar Gashaka, inda maharan suka yi amfani da bindigogi da adduna wajen kai hare-haren.

Rahotanni dai na cewa an kai hare-haren ranar Lahadi daddare har zuwa wayewar garin jiya, amma dai sai a yau ne aka samu karin haske kan lamarin, wanda ya faru a kauyuka dake karamar hukumar Gashaka a yankin tsakiyare jihar ta Taraba.

Rahotanni dai na cewa ko baya ga wadanda aka kashe, da dama daga cikin mutanen kauyukan na yankin Gashaka da aka kai wa hare-hare sun tsere domin gudun hijira, inda suke samun mafaka a wasu garuruwa dake kusa.

Jihar ta Taraba dai ta sha fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini musamman a kananan hukumomin Wukari da Ibi, amma ba kasafai ake samun tarzoma a yankin na Gashaka ba, inmda aka yi kashe-kashen na baya-bayan nan.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti