Naurar tantance amfani da wayar salula a hadarin mota

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An samu karuwa da kashi 840 na yawan tarar da ake sanya wa direbobi

'Yan Majalisar dokoki a birnin New York na Amurka na duba yiwuwar tilasta fara tantance wayar salular direbobin motoci a duk lokacin da aka samu hadarin mota.

Irin wannan gwaji wanda ya yi daidai da yadda ake amfani da na'urar gwajin adadin barasan da mutum ya sha, zai rika nuna ko direba yana amfani da wayar salula a lokacin da hadarin mota ya abku.

Hakan na zuwa ne yayin da jami'ai a New York suka ce an samu karuwa da kashi 840 na yawan tarar da ake sanya wa direbobi don rubuta sakonnin karta kwana a lokacin da suke tuka mota.

An rawaito cewa wani kamfanin kasar Israila ne ke kokarin bunkasa wannan fasaha, kuma ana danganta kamfanin da kokarin da hukumar bincike ta FBI ta yi na bude wayar salular da wani dan bindiga ya yi amfani da ita a San Bernardino.