Lokaci ya yi da za a ceto 'yan matan Chibok — Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta yi kira da babbar murya cewa lokaci ya yi da za a matsawa gwamnati lamba don ganin an ceto 'yan matan Chibok daga hannun kungiyar Boko Haram, tun bayan da suka sace su shekaru biyu da suka gabata.

Amnesty ta kuma ce ya zama wajibi a tallafawa wadanda mayakan Boko Haram din suka ɗaidaita rayuwarsu tare da tabbatar da cewa an kwato musu hakkinsu a shari'ance.

Masu fafutuka na kungiyar Amnesty da sauran kungiyoyi za su bi sahun zanga-zangar lumana da za a yi a Abuja, babban birnin Najeriya da ma sauran kasashe ranar Alhamis domin tunawa da 'yan matan.

A wata sanarwa da kungiyar Amnesty ta fitar, Daraktanta na Najeriya M K Ibrahim ya ce, ''Ba zanga-zangar tunawa da 'yan matan Chibok kawai za a yi ba, ta hada har da ta tunawa da dukkan wadanda kungiyar ta sace ko ta kashe cikin shekaru biyun nan.''

AMnesty ta kuma yi kira da mayakan Boko Haram da su daina kashe fararen hular da basu ji ba basu gani ba, tana mai cewa lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya za ta dauki matakin tabbatar da ƙwaƙƙwaran tsaro da kare rayukan al'umma a yankin arewa maso gabas da ma kasar baki daya.