Hira da iyayen matan Chibok

Hakkin mallakar hoto AFP

A yayin da ake cika shekaru biyu tun bayan sace wasu dalibai daga makarantar sakandaren 'yan mata ta garin Chibok a arewa maso gabashin Najeriya, iyayen wasu daga cikin 'yan na cigaba da bayyani irin halin da suke ciki.

Tun bayan sace 'yan matan na Chibok dai har yanzu babu su babu labarin su, yayin da iyayensu ke ci gaba da rayuwa cikin tashin hankali da taraddadi, da kuma fatan wata rana za su dawo.

Sashen Hausa na BBC zai kawo muku jerin rahotanni na musamman yayin da ake cika shekaru biyu da sace 'yan matan, kuma a yau Abokin aikinmu Abdullahi Kaura Abubakar ya tattauna da biyu daga cikin iyayen 'yan matan da har yanzu suke hannun mayakan Boko Haram, ga kuma yadda hirar su ta kasance.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti