Congo: Yan gudun hijira sun gudu daga sansanoninsu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka sansanonin 'yan gudun hijira biyar a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun zama babu kowa.

Hakan ya faru ne bayan da mutanen dake ciki suka tserewa daga fadan da ake gwabzawa a gabashin kasar.

Mutane fiye da dubu talatin da biyar ne suka bar sansanonin da ke Mpati a arewacin lardin Kivu a cikin makonni uku da suka gabata.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce ta damu matuka game da abinda ya faru ga mutanen.

Ta ce tana samun matsala wajen shiga yankin saboda arangamar da ake yi tsakanin sojojin kasar da kuma kungiyoyin masu rike da makamai.