Yadda mutanen Indiya ke aske gashinsu domin neman albarka

Duk shekara mutane sama da miliyan ke tururuwa wuraren ibadah biyu da ke kudancin Indiya, inda suke fatan a amsa addu'arsu.

Amma duk biyan bukata sai da abun da zaka sadaukar, kuma yawancin masu aikin ibadar na sadaukar da gashinsu ne.

Gopala Amma na matukar bukatar sauya matsalolin da iyalanta ke fama da shi, inda suke neman rasa dan daki dayan da suke ciki a wani kwaroro da ke birnin Chennai a Param Bur.

Duk da Amma tana aikin shara, tana fama da neman na ci da sha.

Bayan da mijinta ya rasa aikinsa ne ya fara shaye-shaye, ga shi babban danta ya koma baya a karatu.

Duk wadannan dalilan ne suka sa Amma ta yi tunanin neman taimakon allolinsu na Hindu.

"Na yanke shawarar zuwa wurin bauta a Tirutanni in kuma aske kaina. Ta haka allolinmu za su sanya min albarka ni da iyalaina," in ji Amma.

Wannan ba karamin aski ba ne, gaba daya gashin nata mai sulbi, da ya kai kimanin inci 32 za a kwashe tas.

Sadaukar da gashin nata gwanin sha'awa da ta yi, ya nuna ta sadaukar da kanta, kuma tana fatan samun albarkar allolinta.

Gashin mutum na da daraja a Indiya, inda yawancin makwabtan Amma na sayar da gashinsu na jikin kum da suka tsefe, ga masu yawo gida-gida suna kasuwancin 'bani gishiri in baka manda,' wadanda ke zuwa sau daya a wata kan kekuna suna kirarin 'zubar kum'.

Sai su bayar don a basu tukwane ko kuma dan kudi kalilan, duba ga nauyin gashin da suka mika, su kuma sai su sayar wa manyan ma'aikatun sarrafa gashi.

Amma gashin da ke makalewa jikin kum na dunkulewa, don haka, wadanda aka aske tas sun fi daraja saboda yana ci gaba da zubowa kamar yana bisa kan asalin mai shi, don haka wani na iya sakawa tamkar nasa ne.

Hakkin mallakar hoto

Tun daga cibiyar hada fina-finai ta Amurka wato Hollywood, zuwa Afrika Ta Kudu, gashin Indiya aka fi amfani da shi, saboda ya fi tsantsi irin kamar gashin turawa, yadda masu gyaran gashi suka fi so.

A Indiya kuwa, kasuwar gashi na samun fiye da dala miliyan 250, a duk shekarar, inda kowanne kilo daya na gashi na samun dala 130, saboda haka gashin Amma, wanda ya kai gram 160, zai kai dala 20 kenan.

Amma wannan bashi da muhimmanci wajen Amma, domin al'adar aske gashi da ake yi saboda addini, na da alaka da tsohon tarihin addinin Hindu.

Akwai tarihin labarin kala-kala, amma duk dai kan allarsu ce Vishnu, wadda aka bige wa kai da adda, hakan kuma ya yi sanadin zubar gashinta a gefe guda.

Daga bisani sai wani mala'ika mai suna Neela Devi ta bata tsiro daya daga nata gashin, inda Vishnu ta yi matukar murna, kuma bayan haka ta sha alwashin biyan bukatun duk wanda ya sadaukar da gashinsa gareta.

Image caption Gida daya baki daya na iya zuwa su sadaukar wa Vishnu da gashinsu.
Image caption Ana zaban ranaku musamman domin ayyukan ibadan, inda wasu ke zuwa domin murnar zagayowar shekarun aure, ko domin neman warakar wata cuta, ko kuma neman iyalansu da albarka.

A jihohin Tamil Nadu da Andhra Pradesh ne ake sarrafa gashi a Indiya, kuma wuraren ibadar biyu na biranen Tirutanni da Tirypati, inda suke amsar gashi tan-tan duk wata.

"Da mai askin ke kwashe min gashin sai na ji duk matsalolina sun wanke," in ji Amma.

Bayan an gama askin sai su shiga dakin ibada da askakken kawunansu, domin samun albarka daga allolin nasu.

Amma ta ce ita ba ta da masaniya kan ko ina gashin nata zai tafi, kuma ko da aka shaida mata cewa gashin nata zai shiga kasuwannin duniya, domin amfanin wasu, sai ta yi dariya.

Ta ce, "Idan har zai kawata wa wani kammani to ai nayi murna sosai," kafin ta fice daga dakin ibadar domin ta kama hanyar gida, da fatan cewa rayuwarta za ta samu ingantacciyar sauyi.