Za mu ceto 'yan matan Chibok — Mansur

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A ranar 14 ga Afrilun 2014 ne aka sace 'yan matan na Chibok

Ministan tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali ya ce suna iya bakin kokarinsu wajen ceto 'yan matan Chibok da Boko Haram ta sace su fiye da 200.

Shekaru biyu ke nan dai da 'yan Boko Haram suka je makarantar sakandare da ke garin Chibok a jihar Borno suka kuma yi awon gaba da 'yan matan.

Mai magana da yawun ministan, Kanar Tukur Gusau, ya ce ministan ya bayyana cewar suna iya ƙoƙarinsu domin kubutar da 'yan matan amma ba za su fadi irin matakan da suke dauka ba saboda halin tsaro.

Sai dai kuma ministan ya ce suna son ceto 'yan matan ne da ransu kuma cikin koshin lafiya.