Ana zanga-zangar cika shekara biyu ta matan chibok

Image caption Kungiyar masu fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok.

A Nigeria,Kungiyar fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok fiye da 200 da kungiyar Boko Haram ta sace daga makarantar kwana da ke garin Chibok a arewa maso gabshin kasar a shekaru biyu da su ka gabata watau Bring Back Our Girls, ta na zanga-zanga a Abuja, babban birnin kasar.

Masu fafutakar dai na rike da kyallaye masu dauke da sakonni da su ke so su isarwa gwamnatin Najeriyar wajen ganin an ceto 'yan matan.

Masu zanga zangar suna wake-wake da rera takensu, suna kuma fatan isar da sako ga shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Ga wasu daga cikin hotunan masu zanga-zanagar:

Image caption Kungiyar masu fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok
Image caption Suna rike da kyallaye masu dauke da sakonni.
Image caption Masu fafutukar na fatan isar da sako ga shugaba Muhammadu Buhari