Wasan tseren jirage marasa matuka zai iya tasiri nan gaba

Wasan tseren jirage marasa matuka a Wembley
Image caption Wasan tseren jirage marasa matuka a filin wasa na Wembley

An fara wani wasan tsere a filin wasa na Wembley a Birtaniya, da ka iya kasancewa gasar wasa da za ta yi fice da samun karbuwa a nan gaba.

Wasu kananan jirage marasa matuka ne suka rika wasan tsere har sai da suka rika zagaya filin wasan.

Irin wannan wasan tsere na da wahalar fafatawar gaske kamar yadda masu sharhi kan wasanni suka bayyana- yana cike da kalubale.

Harabar filin wasan dai ya kasance babu kowa ciki, sai dai dan wani wuri da aka kebe wanda ke cike da manema labarai da aka yiwa kariya da raga.

Ko shakka babu nan da 'yan shekaru kadan dandazon jama'a za su taru don kallon wasan tseren na jirage marasa matuka.

Hukumar wasanni ta Amurka ESPN ta shirya maida wasan tseren jirage marasa matukan wani babban wasan da za a rika kallo ta kafar talabijin.

Amma kuma kafin ta shiryawa masu zuwa kallo kai tsaye tana bukatar shawo kan wasu al'amura, kamar ta yadda za a iya kallon aninhin abinda ke faruwa kai tsayen.