'Za mu magance kauce wa biyan haraji'

Ƙasashen Turai biyar da suka fi ƙarfin tattalin arziki sun amince su yi aiki tare wajen magance kauce wa biyan haraji, sun kuma buƙaci sauran manyan ƙasashe 20 masu ƙarfin tattalin arziki su yi koyi da hakan.

Ƙasashen Birtaniya, da Jamus, da Faransa, da Italiya, da Spaniya za su rika musayar bayanai kan kamfanoni masu asusu a ɓoye.

Sun kuma yanke shawarar saka su a jerin sunayen waɗanda ke gujewa biyan harajin kamar irin su Panama da ba su da bayanai a kan kamfanoni.

Yayinda yake magana a wata ganawa da hukumar lamuni ta duniya IMF a birnin Washington da ke Amurka, sakataren baitulmalin Birtaniya George Osborne ya ce yarjejeniyar wata babbar mahangurba ce ga waɗanda ke kaucewa biyan harajinsu.

Hakan na faruwa ne bayan bankaɗo bayanai kan takardun hada-hadar kuɗi ta Panama.

Amma kuma masu suka na cewa wannan mataki ba zai wadatar wajen shawo kan matsalar kaucewa biyan harajin ba.