Belgium: Ministar sufuri ta yi murabus

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ministan sufuri na Belgium, Ministan sufurin Belgium Jacqueline Galant.

Ministan sufurin Belgium Jacqueline Galant, ta yi murabus sakamakon zargin da ake mata cewa ta yi watsi da wani rahoto da ya nuna rashin cikakken tsaro a filin jiragen saman Belgium gabanin hare-haren kunar bakin waken da aka kai watan jiya a Brussells.

Jam'iyyun adawan Belgium biyu ne suka fitar da rahotan wanda tarayyar Turai ta hada a bara.

Rahotannin sun fiddo da yadda aka nuna halin ko in kula ga harkokin tsaro a filayen jirgin saman, inda suka bayyana kura-kurai da dama kan yanayin kula da lafiya.

Mutane 32 ne suka rasa rayukansu a hare-haren kunar bakin wake da aka kai a filin jirgi na Brussels din a watan Maris.