'Yan Masar na adawa da bai wa Saudiya yankin Maliya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Al-Sisi ya ce dama can tsibirin maliya mallakin Saudiya ne

'Yan sanda a Masar sun harba hayaki mai sa hawaye kan dubban masu zanga-zangar da suke nuna adawa kan hukuncin gwamnatin kasar na mika wa Saudiyya tsibirin Maliya.

An dai haramta yin zanga-zanga a birnin Al-Kahira, amma masu zanga-zangar sun mamaye kan tituna duk kuwa da irin gargadin da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta yi.

masu zanga-zangar dai sun fito ne daga bangarorin masu sassaucin ra;ayi da masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama, wadanda suke zargin shugaba Abdel Fattah al-Sisi da sayar da tsibiran don neman Saudiya ta zuba jari a kasar.

Amma gwamnatin ta ce dama can tsibiran mallakin Saudiya ne, an bai wa Masar aronsu ne na dan lokaci.

Karin bayani