'Akwai yaudara a tallan Internet'

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan majalisar dokokin Birtaniya 50 sun ce, akwai yaudara cikin yadda kamfanoni ke tallar Internet mai matuƙar inganci.

Sai dai duk da haka kamfanonin dake samar da Internet ba su karya doka ba.

Amma wasu ƙungiyoyi na kiran a tilastawa kamfanoni su rika yin gaskiya.

Koda hukumar dake sa ido akan yadda ake tallace-tallace ta ce, ta na sane da ƙorafin jama'a akan rashin gaskiya wajen tallata sauri da ƙarfin Internet da ake samarwa.

Ƙungiyoyin sun nemi a baiwa jama'a ƙarin ikon neman haƙƙinsu idan har Internet din da ake samar musu ba ta kai ingancin abinda ake tallatawa ba.