Kano: Yara huɗu sun mutu a cikin mota

Image caption Abdullahi Ganduje, Gwamnan Kano

A Kano an gano gawawwakin wasu yara huɗu da suka rasu sakamakon kullewa a cikin mota.

Lamarin ya auku ne a unguwar Sharaɗa inda yaran maza masu shekaru uku zuwa biyar suka shiga motar da aka ajiye a wani kango.

Yaran sun yi ta yunƙurin fitowa daga cikin motar, ba tare da nasara ba, har tsawon wani lokaci.

Kakakin runudunar 'yan sandan jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya ya ce, ana kyautata zaton yaran sun shiga motar ne tun misalin ƙarfe 11 na safe, amma sai misalin ƙarfe 5:30 na yamma aka gano su.

'Yan sanda sun ce, yaran sun mutu ne sakamakon zafi da rashin iska a cikin motar.

Tuni dai iyayen yaran suka soma karɓar masu gaisuwar jajenta musu wannan rashi.