Manchester City za ta kara da Real Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty

Manchester City za ta kara da Real Madrid a wasan daf da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

Wannan na nufin cewa City za ta iya fuskanci sabon kocinta mai jiran gado Pep Guardiola, a wasan karshe.

Guardiola zai maye gurbin tsohon kociyan City Manuel Pelligrini a lokacin bazara.

Za a yi wasan zagaye na farko a filin wasa na Etihad da ke Manchester ranar 26 ga watan Afrilu, a kuma yi zagaye na biyu a babban birnin Sipaniya ranar 4 ga watan Mayu.