Najeriya: Bayan Chibok akwai Damasak

Hakkin mallakar hoto

Duk da cewa hankulla sun karkata ga sace matan Chibok bayanai na nuna cewa, koda a Damasak an sace yara da dama.

Koda shekara daya bayan sace 'yan matan Chibok akalla yara 300 ne aka sace a Damasak.

Bayanai na nuna cewa, 'yan Boko Haram sun sace mata da kananan yara a garuruwa da dama a yankin arewa maso gabas.

Dubban 'yan mata ne aka tilasta wa gudanar da rayuwarsu tare da 'yan boko haram.

Wasu sun aure su, da kuma bin turbar koyarwarsu ta ayyuka na 'yan Boko haram.

Yanzu shekaru biyu kenan tun bayan sace 'yan mata 219 daga yankin Chibok na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya da kungiyar Boko Haram ta yi.