Malick Sidibe ya rasu

Ana ci gaba da jajen mutuwar fitaccen mai ɗaukar hoto dan Mali, Malick Sidibe, wanda ya rasu yana da shekaru 80.

Shi dai Sidibe ya rasu ranar Alhamis, kuma ya yi fice a duniya saboda hotunan dake nuna rayuwar 'yan ƙasar Mali.

Yawancin hotunansa ba masu launi ba ne, kuma suna nuna rayuwa a Mali a shekarun 1960 zuwa 1970.

Manazarta hotuna sun ce, hotunan da ya ɗauka sune suka nunawa duniya rayuwa a yammacin Afirka bayan mulkin mallaka.

A shekara ta 2007 ya zama ɗan Afirka na farko da ya lashe lambar yabon masu ɗaukar hoto ta Golden Lion.

Jama'a a faɗin duniya sun yi amfani da shafin Twitter wajen yaba rayuwarsa da kuma tasirinsa a fagen ɗaukar hoto a duniya.