EU:Sabon babin dangantaka da Iran

Hakkin mallakar hoto ISNA

Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta ce kungiyar EU na shata sabon babin dangantaka da Iran.

Ta na magana ne yayin wata ziyara da ta kai Tehran bayan yarjejeniyar nukiliya da aka cimma a bara tsakanin Iran da manyan kassashen duniya.

Tawagar Ms Mogherini za ta tattauna batutuwan cinikayya da makamashi da kuma sauran al'amura da mahukuntan na Iran.

Sai dai kuma a bayan fage akwai damuwa da kuma rashin jituwa.

Manyan bankunan turai da kamfanoni na ci gaba da nuna dari dari wajen zuba jari a Iran inda har yanzu takunkumin da Amurka ta sanyawa kasar dangane da zargin ayyukan ta'addanci da keta haddin bil Adama ke cigaba