Japan:Lokaci na kurewa masu aikin ceto

Hakkin mallakar hoto AFP

Firaministan Japan Shinzo Abe ya yi gargadin cewa masu aikin ceto na fuskantar babban kalubale na kurewar lokaci a kokarin da suke yi na kai wa ga mutanen da suka makale cikin baraguzai a girgizar kasa har guda biyu da suka auku a kudancin tsibirin Kyushu.

Mr Abe yace akwai matukar bukatar gaggautawa saboda hasashen yiwuwar guguwa mai karfi hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya, lamarin da ya sanya fargabar aukuwar zabtarewar kasa.

Dubban sojoji na taimakawa laluben baraguzan gine gine domin gano mutane kusan 100 daya wadanda har yanzu ba a san inda suke ba.

Lalacewar tituna da gadoji na kassara yunkurin isa ga al'umomin da ke yankunan tsaunuka masu nisa.

A kalla mutane 32 aka tabbatar sun mutu a girgizar kasar.