'Za mu ceto 'yan matan Chibok a raye'

Rundunar sojan sama ta Nigeria ta bayyana cewa tana da ƙwarin gwiwar za a gano 'yan matan nan 'yan makarantar Chibok.

Ta kuma nanata cewa za a ceto su a raye, sakamkon nasarar da ta ce dakarun tsaro na samu kan 'yan Boko Haram.

Sojan saman sun kuma ce, za su tsaurara sintiri ta sama da ta ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne yayin da 'yan matan suka cika shekaru biyu a hannun 'yan kungiyar Boko Haram.

A ciki da wajen Nigeria ana ci gaba da kiran a ceto 'yan matan na Chibok su fiye da ɗari biyu.