Zamu gano yammatan Chibok a raye— Air Vice Marshal Sadique

Image caption Air Vice Marshal Sadique ya ce za a gano yammatan Chibok a raye

Rundunar sojan sama ta Najeriya ta bayyana cewa ta na da kwarin gwiwar cewa za a gano 'yan matan nan 'yan makarantar Chibok, kuma a ceto su a raye, sakamakon nasarar da ta ce dakarun tsaro ke samu kan 'yan Boko Haram da kuma tsaurara sintiri ta sama da kasa da ake yi.

Wannan dai na zuwa ne yayin da 'yan matan suka cika shekaru biyu a hannun 'yan Boko Haram wadanda ke garkuwa da su.

Air Vice Marshall Sadique Abubakar, shi ne babban hafsan sojin sama na Najeriya, kuma wakilinmu a Bauchi, Ishaq Khalid ya tambaye shi, ko shin ko wanne hali ake ciki game da ceto 'yan matan daga hannun Boko Haram?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti