Sabon yunƙurin kawar da cutar Polio

Daga yau ne ƙasashe fiye da 150 zasu soma amfani da riga kafin cutar shan inna, a sabon matakin kawar da cutar baki ɗaya.

Cutar ba ta da magani tana haddasa shanyewar ɓangaren jiki, kuma tana iya zama barazana ga rayuwar mutum.

Cikin 'yan shekarun nan mutane ƙalilan ne suka kamu da cutar ta Polio.

Amma hukumar lafiya duniya wato WHO tana fargabar cewa, cutar za ta iya sake yaɗuwa cikin gaggawa idan har ba a ɗau matakan kawar da ita ba.

WHO ta ce, yanzu a ƙasashen Afghanistan da Pakistan ne cutar ta shan inna ke yaɗuwa.

A shekarar 1988 ƙasashe 125 ne ka fama da matsalar cutar ta Polio.

Bara hukumomin Nigeria suka ce, anyi shekara guda ba tare da wani ya kuma da cutar ba.